


A jiya ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ziyaraci Monaca, inda ya tattauna da yarima Albert II, kana shugaban masarautar Monaco, a wani mataki na karfafa alakar kasashen Sin da Monaco.
A jawabinsa, shugaba Xi ya ce kasashen Sin da Monaco, sun kafa wani kyakkyawan misali na musayar abokantaka tsakanin kasashen da suka sha bambanta a fannin girma da tarihi da al'adu da ma tsarin zaman rayuwar jama'a.
Ya ce, bangarorin biyu sun rungumi tsarin bude kofa da yin hadin gwiwa da kara amfana da juna. Ya kara da cewa, kasar Sin tana maraba da Monaco da ta shiga a dama da ita wajen raya shawarar ziri daya da hanya daya.
Shugaba Xi ya kuma bukaci sassan biyu, da su daga matsayin alakarsu a fannin kare muhalli, kana kasar Sin tana maraba da gidauniyar yarima Albert II da ta gudanar da ayyukanta na taimakawa jama'a a kasarsa da nufin kare muhalli, ta yadda za a bunkasa musayar al'adu da ta jama'a tsakanin al'ummomin kasashen biyu.
A nasa jawabin yarima Albert II ya bayyana ziyarar shugaba Xi a matsayin ziyara ta tarihi. Ya kuma bayyana kudurin kasarsa na fadada alaka da kasar Sin a fannoni, kamar kimiyya, da fasahar kere-kere, da kirkire-kirkire, da muhallin halittu da kare muhalli da namun daji da kuma makamashin da ake iya sabuntawa.
Ziyarar aikin da shugaba Xi ya kai a Monaco, ita ce ta farko da wani shugaban kasar Sin ya kai kasar dake nahiyar Turai (Ibrahim)








