in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ya kafa dokar haramta boye kudaden kasar
2019-03-22 10:45:43 cri

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir a ranar Alhamis ya fitar da dokar gaggawa ta haramta boye kudaden kasar da cinikin bunburutu.

Wata sanarwa daga ofishin shugaban kasar ta Sudan ta ce, dokar ta haramta yin dabaru na cinikayyar kudi domin haifar da illa ga darajar kudin kasa ko boye kudaden a wajen bankuna da nufin yin bunburutunsu.

Umarnin dokar ya haramta mallaka ko kuma boye kudaden kasar sama da pound miliyan 1 ga daidaikun mutane ko kuma pound miliyan 5 ga kamfanoni masu zaman kansu, in ji sanarwar.

A cewarsa samarwar, wadanda suka take dokar, za su fuskanci zaman gidan yari na tsawon watanni 6 zuwa shekaru 10, da kuma biyan tara da fuskantar tuhumar karkatar da kudaden kasar ba bisa ka'ida ba.

A ranar 22 ga watan Fabrairu, al-Bashir ya kafa dokar ta baci a duk fadin kasar ta Sudan na tsawon shekara guda bayan da zanga zanga ta barke a kasar a watan Disambar shekarar bara sakamakon matsalar da 'yan kasar ke kokawa na tabarbarewar tattalin arziki da tsadar kayayyakin masarufi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China