Shugaban Sudan ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da Mikhail Bogdanov, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha kuma wakilin musamman kan batun yankin Gabas ta Tsakiya a wannan rana a birnin Khartoum, babban birnin kasar.
Bisa sanarwar da fadar shugaban kasar Sudan ta bayar, an ce, a yayin ganawar, shugaba al-Bashir ya ce, inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 a fannonin siyasa, tattalin arziki da cinikayya ya dace da moriyarsu duka.
Mikhail Bogdanov ya yiwa kafofin yada labaru bayani bayan ganawar cewa, bangarorin 2 sun tattauna hadin gwiwar dake tsakanin Rasha da Sudan ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, da kuma baiwa jami'an Sudan horo da makamantansu. Haka kuma, kasar Rasha za ta karfafa huldar dake tsakaninta da Sudan ta fuskar siyasa, tattalin arziki da ciniki, ta kuma yaba da matsayin da Sudan ke tsayawa a kai na sanin ya kamata kuma cikin daidaito kan batutuwan kasa da kasa, da batun Afirka da na yankin Gabas ta Tsakiya. (Tasallah Yuan)