Tawagar ta Amurka ta halarci taron tattaunawar a ranar Lahadi tare da shugabannin majalisar dokokin kasar Sudan a Khartoum, babban birnin kasar.
"Nayi matukar farin ciki yayin da na ga mutane a nan Sudan suna da 'yancin yin bauta," inji Gus M. Bilirakis, shugaban sashen tabbatar da 'yancin dan adam ta majalisar dokokin Amurka, kana shugaban tawagar wakilan na Amurka.
Bilirakis, ya kara da cewa, ya yabawa hadin kan dake tsakanin kasar Sudan da kasarsa ta fuskar yaki da ta'addanci.
Kakakin majalisar dokokin kasar Sudan Ibrahim Ahmed Omer, ya jaddada muhimmancin ziyarar tawagar wakilan na Amurka zuwa kasar Sudan.
An fara muhimmiyar ganawa da wakilan na Amurka ne tun daga ranar Asabar tsakanin jami'an gwamnatin Sudan da shugabannin 'yan adawar kasar.