Rahoton kamfanin dillancin labarai na kasar Sudan SUNA, ya ruwaito cewa, an kafa kotunan ne bisa umarnin gaggawa da shugaban kasar Omar al-Bashir ya bayar a ranar Litinin.
A cewar rahoton, an dorawa kotunan alhakin yanke hukunci kan wadanda suka take tanadin dokar manyan laifuffuka na 1991 da dokar ta baci da tsaron kasa da kuma dokokin gaggawa da shugaban kasar ya ayyana ko kuma wani laifi da ya sabawa kowacce doka.
A ranar 22 ga watan nan ne shugaba al-Bashir ya ayyana dokar ta baci a fadin kasar na tsawon shekara 1, biyo bayan zanga-zangar da ake yi a kasar tun daga ranar 19 ga watan Disamban bara, game da tabarbarewar yanayin tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki. (Fa'iza Mustapha)