Rahotanni daga Sudan ta kudu na cewa, ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar ya ba da gudummawar magungunan zazzabin cizon sauro na malaria da kudinsu ya kai sama da Yuan miliyan biyar, domin kara karfin kasar na yakar cututtuka da ake samu a yankuna masu zafi.
Jakadan kasar Sin a Sudan ta kudu He Xiangdong, ya bayyana cewa, magungunan za su taimaka wajen kara karfin kasar na tunkarar barkewar zazzabin malaria da ma inganta bangaren kiwon lafiyar kasar.
Jami'in na kasar Sin ya ce, kasarsa za ta ci gaba da taimakawa bangaren kiwon lafiyar kasar ta hanyar horas da ma'aikatan kiwon lafiya.
A nasa jawabin ministan kudin kasar Sudan ta kudu Salvatore Garang wanda ya karbi gudummawar magungunan a jiya Alhamis, ya yabawa kokarin kasar Sin na taimakawa kasar da yaki ya wargaza, yana mai cewa, kasarsa na son karfafa alaka da kasar Sin a fannoni kamar na cinikayya da raya kasa da kuma fannin Ilimi.(Ibrahim)