Shirin samar da abinci na MDD (WFP), ya yabawa gwamnatin kasar Sin sakamakon tallafin abinci da take da shi ga mutane marasa galihu a Sudan ta kudu.
Valerie Guarnieri, mataimakiyar babban daraktan gudanarwar shirin WFP, ta ce a halin yanzu sama da mutane miliyan 7 ne suke bukatar abinci a Sudan ta kudu, kana taimakon abincin da kasar Sin ta bayar na kwanan nan zai ceto rayukan dubban mutane daga matsananciyar yunwa da rashin abinci da suke fama da shi.
Guarnieri ta ce, shirin samar da tallafi na hadin gwiwa wanda gwamnatin Sudan ta kudu ta kaddamar da shi, kasar Sin da shirin WFP a shirye suke su kawo karshen matsalar karancin abinci a kasar ta gabashin Afrika.
Da take jawabi a Juba a lokacin bikin mika tallafin shinkafa wanda kasar Sin ta mikawa hukumar MDDr, yawansa ya kai tan 2,048. Gudumowar wani bangare ne daga cikin tan 8,800 na shinkafa wanda Sin ta yi alkawarin baiwa Sudan ta kudun tun a shekarar 2017 don kawar da matsalar mummunan karancin abinci.
He Xiangdong, jakadan kasar Sin a Sudan ta kudu, ya ce wannan taimakon wani bangare ne na kokarin da gwamnatin Sin ke yi na tallafawa jaririyar kasar domin kawo karshen matsanancin halin da al'umma ke ciki a kasar.
He ya ce, "Idan za mu iya aiki tare, za mu iya ceto rayuka, kuma za mu iya samar da sauyi ga rayuwar jama'a".(Ahmad Fagam)