Hukumomi a Sudan ta kudu sun ce, wasan marathon da ake ci gaba da gudanarwa a kasar a bikin ranar hadin kan kasar karo na hudu, zai taimakawa kasar wajen farfadowar zaman lafiya da hadin kai, kuma zai taimaka wajen kawo karshen yakin basasar kasar wanda aka shafe shekaru 5 ana gwabzawa.
Mataimakin shugaban kasar James Wani Igga ya bayyana wasan na marathon wanda ya samu tallafin shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar Sudan ta kudu wato UNMISS cewa, zai taimaka wajen karfafa zaman lafiya da hadin kai a tsakanin kabilun kasar 64.
Tawagogin 'yan wasan sun fito ne daga tsoffin yankuna 10 na kasar ta gabashin Afrika, tun gabanin barkewar tashin hankalin kasar.
David Shearer, wakilin musamman na babban sakataren MDD kana shugaban tawagar UNMISS ya ce, yana fata ranar hadin kan kasar za ta haifar da gagarumin ci gaba wajen aiwatar da yarjejeniyar farfadowar zaman lafiya a kasar.
Ya yabawa bangarorin masu adawa na kasar bisa kwarin gwiwar da suka nuna na amincewar da suka yi, inda suka halarci taron aza tubalin wanzar da zaman lafiyar kasar ta Sudan ta kudu.
Shearer ya ce, mafi yawa daga cikin mutanen da rikicin ya tilastawa ficewa daga gidajensu suna bukatar komawa gidajensu yayin da ake samun ci gaba ta fuskar farfadowar zaman lafiya a kasar.
Ya kara da cewa, ana fata a bikin ranar hadin kan kasar na shekara mai zuwa, za'a kara samun kyautatuwar zaman lafiya, kana sabuwar gwamnatin kasar mai zuwa za ta dora daga inda aka tsaya don ciyar da kasar Sudan ta kudu gaba.(Ahmad Fagam)