A jiya Laraba Sudan ta kudu ta sanar da cewa, tana ci gaba da gina wani tsari wanda zai taimaka wajen raba dukkan jama'ar kasar da makamai a wani mataki na kawo karshen yaduwar kananan makamai a fadin kasar.
Laftanar janar Andrew Kuol Nyuon, shugaban hukumar dake kula da tsaron al'umma da hana yaduwar kananan makamai na Sudan ta kudu, ya bayyana cewa, horas da jami'an tabbatar da bin doka da oda, da samar musu da cikakkiyar kwarewa, zai taimaka wajen wayar da kan jama'a game da zaman lafiya da kuma hana yaduwar makamai a cikin kasar.
"Za mu ci gaba da karadewa dukkan jihohi domin wayar da kan jama'a a kasarmu, domin a samu saukin raba jama'a da makamai. Idan ba mu sauya tunanin mutane game da illar rike makamai ba, to ba za mu iya raba su da makaman dake hannayensu ba," in ji Nyuon.(Ahmad Fagam)