Ya kuma kara da cewa, kasar Sin za ta fara aiwatar da batutuwan da shugabannin kasashen biyu suka cimma ra'ayi daya kansu cikin sauri, kuma za ta aiwatar da su yadda ya kamata.
A daren ranar 1 ga wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump suka gana a birnin Buenos Aires, fadar mulkin kasar Argentina. A yayin ganawar tasu, shugabannin biyu sun bukaci wakilan tawagogin tattalin arziki da cinikayya na kasashensu, da su gaggauta yin shawarwari domin cimma yarjejeniya, da nufin soke matakan kara haraji da bangarorin biyu suka dauka tun shakarar bana, ta yadda za a samu daidaito a tsakaninsu a fannin ciniki da kuma cimma moriyar juna. (Maryam)