in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na gudanar da nazari kan matakan da Amurka za ta dauka wajen kayyade fitar da fasahohinta zuwa ketare
2018-11-23 16:17:17 cri
Kwanakin baya, kasar Amurka ta fidda wata sanarwa, inda take neman ra'ayoyin jama'a kan karfafa matakan kayyade fitar da fasahohi guda 14 zuwa ketare. Dangane da wannan lamari, kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya bayyana a jiya Alhamis cewa, kasar Sin ta lura da wannan sanarwa, kuma a halin yanzu, tana kimanta matakan da mai yiyuwa kasar Amurka za ta dauka.

Gao Feng ya ce, tsaron kasa ya samu ne ta hanyar bude kofa ga waje, kafa shingayen ciniki ba zai ba da taimako wajen tabbatar da tsaro da kuma raya cinikayyar kasa ba. Ya kara da cewa, ana fatan kasar Amurka za ta iya daukar matakan da za su dace domin kyautata yanayin cinikin duniya, yayin samar wa kanta damammaki wajen fitar da hajojinta masu inganci ta yadda za ta rage gibin cinikayyar kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China