Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin ta amsa tambayoyi game da jawabin mataimakin shugaban Amurka
Mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya yi jawabi a gun taron shugabannin masana'antu da cinikayya na kungiyar APEC, inda ya gabatar da ra'ayin dake shafar kasar Sin, yana mai cewa, gudummawar da kasar Sin ta baiwa kasashen tsibiran tekun Pasifik sun haifar da tarin basussuka a kan kasashen. Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyanawa 'yan jarida a yau cewa, kasar Sin na hada gwiwa da kasashe da dama a duniya bisa tushen girmamawa da samun moriyar juna. Kuma yayin da kasar Sin take kokarin raya hadin gwiwar, tana bin ra'ayin samun moriyar da ta dace da nuna gaskiya da sahihanci da kuma girmama bukatun gwamnatocin kasashen da suka samu gudummawa daga gare ta. Ta ce babu wata kasa da ta shiga mawuyacin hali saboda basussuka sanadiyyar hadin gwiwarta da kasar Sin, har ila yau, ta ce hadin gwiwa da kasar Sin ya inganta karfin kasashen na samun bunkasuwa da kansu da kyautata zaman rayuwar jama'arsu.
Hua ta kara da cewa, ana ba da shawara ga kasar da abin ya shafa da ta daina zargin sauran kasashe, ta cika alkawarinta yadda ya kamata, da yin adalci ga kasashe manya ko kanana, da girmama zabin sauran kasashen na samun bunkasuwa bisa halin da ake ciki, da kuma gudanar da ayyukan sa kaimi ga samun bunkasar kasashe masu tasowa. (Zainab)