Wata kididdiga da baitul malin Amurka ta fitar, ta nuna cewa, jimilar kudin lamunin Amurka na kasar Sin, ta kai dala triliyan 1.151 a watan Satumba, wanda ya sauka da dala triliyan 13.7 daga watan Augusta. kididdigar ta nuna cewa, Japan,wadda ita ce ta biyu wajen sayen lamunin,ta koma mai saidawa a watan Satumba,inda jimilar dukiyarta ta sauka daga triliyan 1.03 zuwa 1.028.
Bayyanan sun yi bayani ne kan saye da sayarwar lamunin tsakanin hukumomin kasashen ketare da masu sayen hannayen jari masu zaman kansu. Baki daya dai, kudin lamunin Amurka a kasashen ketare ya tsaya ne kan dala biliyan 29.1 a watan Satumba. (Fa'iza Mustapha)