Vera Songwe, wadda ta ce galibin kasashen Afrika na fuskantar kalubale iri guda, a wani yanayi da ba a taba fuskanta ba a duniya, ta bayyana kudurin hukumarta na cike gibin da ke akwai wajen magance matsalolin da nahiyar ke fuskanta.
Da take yi wa jakadun kasashen Afrika bayani game da ayyukan hukumar, ta ce ta hanyar aiki tare da kasashe mambobinta wajen tuntuba da aiwatar da ingantaccen bincike da samar da sakamako, hukumar za ta samar da mafitar da za ta gaggauta cimma burin da nahiyar ke son cimmawa zuwa shekarar 2063 da kuma maradun duniya da ake son cimmawa ya zuwa 2030.
Samar da hanyoyin samun ci gaba mai dorewa don gaggauta baza komar tattalin arzikin nahiyar Afrika da inganta ayyukan masana'antu da samar da hanyoyin kirkire-kirkire don samun kudin aiwatar da ayyukan more rayuwa, na daga cikin muhimman bangarorin da ta lashin hukumar za ta taimakawa kasashe mambobinta. (Fa'iza Mustapha)