Jiya Laraba 17 ga wata, ma'aikatar harkokin kudi ta kasar Amurka ta fitar da rahoto kan manufar darajar kudin musaya na farkon rabin shekarar bana, inda take ganin cewa, kasar Sin ba ta tsoma baki kan batun darajar kudin musaya ba domin neman samun fifiko wajen cinikayya. Wannan shi ne karo na hudu da ma'aikatar ta tabbatar da batun tun bayan da Donald Trump ya zama shugaban kasar.
A ran nan kuma, ma'aikatar harkokin kudin Amurka ta fitar da rahoto kan tattalin arzikin duniya da manufar darajar kudin musaya, inda take ganin cewa, dukkan muhimman abokan cinikayyar Amurka ba su taba tsoma baki kan darajar kudin musaya ba, amma ta shigar da kasashen Sin da Japan da Jamus da Koriya ta Kudu da Switzerland da ma Indiya cikin sunayen wadanda za a sanya musu ido kan manufar.
Ma'aikatar ta kuma nuna cewa, Amurka tana dora matukar muhimmanci kan alkawarin da kasar Sin ta yi na hana faduwar darajar kudi don yin takara, kuma za ta ci gaba da maida hankali kan hawa da saukar darajar kudin musayar kasar Sin, da kuma kiyaye tuntuba tare da Bankin Jama'ar kasar Sin. Amurka na ganin cewa, aikin gyaran tattalin arziki da kasar Sin ke gudanarwa don yada amfanin kasuwa zai karfafa zukatan masu zuba jari ga kudin Sin na RMB.(Kande Gao)