Dangane da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, kasar Sin daya tak ce a duniya, kuma yankin Taiwan wani bangare ne na kasar Sin, wanda ba za a iya raba shi daga kasar ba. Haka kuma Tekun Kudancin Sin da ma yankin teku dake kusa da su mallakar kasar Sin ce. Kasar Sin tana mai da hankali kwarai kan kiyaye da kuma raya harkokin hakkin dan Adam. Haka kuma, al'ummomin kasar Sin suna da 'yancin bin kowane irin addini bisa dokar kasar. (Maryam)