Sin ta mai da martani ga Amurka ne don kare muradunta, ba don tsoma baki cikin harkokin gidan Amurka ba
Kwanan baya, kasar Amurka ta yi zargin cewa, kasar Sin tana tsoma baki a harkokin gidan kasar Amurka a yayin da take mai da martani kan takaddamar ciniki dake tsakaninta da kasar Amurka. Dangane da wannan harka, kakakin ma'aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya bayyana a jiya Alhamis cewa, duk matakan da kasar Sin ta dauka tana yi ne don kare muradunta da kuma kiyaye tsarin cinikin tsakanin kasa da kasa, kuma ko kadan ba ta son tsoma baki a cikin harkokin gidan kasar Amurka.
Ya kuma jaddada cewa, kasar Amurka ce ta tayar da takaddamar ciniki tsakaninta da kasar Sin, amma kasar Sin ba ta son yin haka, domin kiyaye hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannin cinikayya. Har zuwa yanzu, kasar Sin tana son raya dangantakar cinikayya dake tsakaninta da kasar Amurka, a sa'i daya kuma, tana tsayawa tsayin daka wajen kare muradunta. (Maryam)