Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana a ranar Talata cewa, kasashen Amurka da Sin suna da kyakkyawar alaka a tsakaninsu, don haka akwai bukatar Amurkar ta kara kwazo wajen inganta wannan alaka.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Heather Nauert ta bayyana hakan ne yayin da take amsa tambayar da aka yi mata a taron manema labarai da aka saba shiryawa kan yadda za ta bayyana matsayin alakar kasashen biyu.
Ta bayyana kasar Sin a matsayin mai takara, tana mai cewa, alakar sassan biyu tana da sarkakiya, kana sassan biyu suna da muradu iri daya a wasu sassa, ciki har da batun kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya. Sai dai kuma, a cewarsa, ra'ayoyin kasashen biyu sun sha bamban kan wasu batutuwa, amma duk da haka za su ci gaba da hada kai har sai haka ta cimma ruwa.(Ibrahim)