Tun daga yau kasar Sin ta fara rage harajin kwastam da take bugawa wasu nau'o'in hajjoji 1585 da take shigowa dasu
Bisa sanarwar da kwamitin kula da manufofin buga harajin kwastam na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar a kwanakin baya, tun daga yau wato ranar 1 ga watan Nuwambar nan, kasar zata fara rage adadin yawan harajin kwastam da take bugawa wasu hajjojin kasashe, ciki har da kayan saka, da na'urorin lantarki da bangarorinsu, wadanda suka shafi nau'ikan haraji guda 1585, kana, adadin yawan harajin da aka buga ya ragu daga kashi 10.5 bisa dari zuwa kashi 7.8 bisa dari.
Kwararru na ganin cewa, rage harajin kwastam a wannan karo zai taimaka ga kyautata tsarin sana'o'in kasar Sin, da rage yawan kudaden da kamfanonin zasu kashe, da kuma biyan bukatun masu sayayya na yau da kullum, al'amarin da yake kara nunawa duniya niyyar kasar Sin ta cigaba da fadada bude kofarta ga kasashen waje.(Murtala Zhang)