Jiya Litinin, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jagoranci taron majalisar gudanarwar kasar, inda ya tabbatar da daukar matakan inganta tsarin mayar da harajin hajojin da ake fitarwa daga kasar, domin saukaka gudanar da kasuwanci, da bunkasa hada-hadar cinikayyar kasashen waje. Har wa yau, firaministan ya gabatar da muhimman tsarin ayyukan kyautata tsoffin unguwanni, a wani kokari na inganta zaman rayuwar mutanen dake fama da talauci.
Taron ya nuna cewa, inganta tsarin mayar da harajin hajojin da ake fitarwa daga kasar, na dacewa da ka'idojin hukumar WTO. Kana kuma, kara inganta tsarin mayar da harajin hajojin da ake fitarwa daga kasar zai taimaka sosai, wajen zurfafa ayyukan yin gyare-gyare ga bangaren samar da kayayyaki, da shawo kan kalubalolin da ake fuskanta a duniya, tare kuma da raya hada-hadar cinikayyar kasashen waje ta hanyar da ta dace. (Murtala Zhang)