Duk dai da irin kiraye kiraye da sassan 'yan kasuwa, da kungiyoyi tare da kwararru suka ta yi, a ranar Alhamis shugaban Amurka Donald Trump, ya sanya hannu kan wata takardar amincewa da kakabawa hajojin kasar Sin da suka kai dala biliyan 60 dake shiga Amurka haraji, tare kuma da wasu takunkumi da zai shafi jarin da Sin din ke zubawa a kasarsa.
A daya bangaren kuma, mashawarci ga fadar White House game da harkokin cinikayya ya shaidawa manema labarai cewa, kasar Sin za ta fuskanci matsala idan har ta ce za ta dauki fansa kan wadannan matakai na Amurka.
Game da hakan, Madam Hua ta ce wadannan kalamai na jami'in Amurkar kuskure ne, sun kuma nuna irin rashin fahimtar sa ga niyyar kasar Sin da karfinta na kare moriyarta ta halal. Kaza lika jami'in bai hango irin illar da Amurkar za ta fuskanta a sakamakon yadda ta kare aniyarta wajen daukar matakan ba.