in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta gabatarwa WTO korafi game da harajin da Amurka ta sanyawa kayayyakin kasar Sin da ya kai dala biliyan 16
2018-08-23 13:53:29 cri
A yau Alhamis kasar Sin ta bayyana aniyarta na mika kokenta a gaban hukumar ciniki ta duniya (WTO), dangane da matakin Amurka na sanya kudin haraji kan kayayyakin kasar Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 16 karkashin doka mai lamba 301, kamar yadda ma'aikatar ciniki ta kasar Sin (MOC) ta tabbatar da hakan.

A wata sanarwar da kakakin na MOC ya sanar ta shafin intanet, yace, sakamakon shigar da korafin da tayi gaban hukumar sasanto dake karkashin kungiyar WTO, kasar Sin tana fatan kiyaye matsayin ciniki cikin 'yanci da kuma matsayin tsarin cinikayya na gamayyar kasa da kasa domin kare hakkokinta da moriyarta.

"Kasar Sin ta yi Allah wadai da wannan mataki, kuma zata dauki matakan da suka dace na mayar da martani, a cewar sanarwar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China