in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan Amurka za ta mutunta hadin-gwiwar da ake yi tsakanin Sin da sauran kasashe masu tasowa
2018-10-17 19:27:58 cri
Game da zargin da kasar Amurka ta yi wa kasar Sin, na cewa wai Sin na yunkurin kara fadada tasirin ta a duniya, ta hanyar baiwa sauran kasashe basussuka, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a yau Laraba cewa, kasar Sin ta yi abun da ya dace, yayin da take gudanar da hadin-gwiwa tare da sauran kasashen masu tasowa, kana ba ta taba gindaya duk wani sharadin siyasa ba, yayin da take tallafawa sauran kasashen duniya.

Lu Kang ya ce, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba, Amurka na furta kalaman rashin gaskiya, domin biyan bukatunta ta fuskar siyasa, al'amarin da ke sanya kasar Sin matukar takaici. Ya ce Sin na bukatar Amurka, da ta mutunta hadin-gwiwar ta da Sin, da ma sauran kasashe masu tasowa. Kana ta bayar da gudummawar ta ga ci gaban wadannan kasashe, maimakon yunkurin raba tsakanin Sin da sauran kasashe masu tasowa. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China