Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Madam Hua Chunying ta maida martani game da wannan wasika, inda ta ce, nuna ra'ayin bada kariya ga harkokin cinikayya da Amurka ta yi, bai dace da dokokin kasashen duniya ba, kana, kamar yadda malam Bahaushe kan ce, kowa ya shuka zamba, shi zai girba.
An ce, akwai masana tattalin arziki sama da 1100, wadanda suka sa hannu kan wannan wasika, inda suka bayyana cewa, kara sanya haraji kuskure ne babba da Amurka ta tafka, wanda zai tsawwala farashin kaya, kuma masu sayayya a Amurka za su sha wahala. Har wa yau, kara sanya harajin kwastam zai kawo illa ga dangantakar dake tsakanin Amurka da sauran wasu kasashe, lamarin da ba zai taimaka ga shimfida zaman lafiya a duk fadin duniya ba.(Murtala Zhang)