Kakakin ya ce, ba za a amince da wannan takardar jerin kayayyakin da za'a sanyawa haraji da Amurka ta fitar ba, kuma ana nuna babbar adawa da hakan. Ya ce abun da Amurka ta yi, na kawo babbar illa ga kasar Sin da ma duk duniya, har ma tana lahanta kanta.
Kakakin ya kara da cewa, kasar Sin na matukar mamaki game da abun da Amurka ta yi. Kuma domin kare muradun kasa gami da moriyar jama'arta, gwamnatin kasar za ta mayar da martani. Har wa yau kuma, Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su yi kokarin kare manufofin gudanar da cinikayya cikin 'yanci, da tsarin cinikayya dake kunshe da bangarori daban-daban. Bugu da kari, Sin za ta kara kai karar Amurka a gaban kungiyar kasuwanci ta kasa da kasa WTO, game da wannan batu.(Murtala Zhang)