Cibiyar musanyar tattalin arzikin kasar Sin da kungiyar 'yan kasuwa ta kasar Amurka sun gudanar da shawarwari karo na goma tsakanin shugabannin 'yan kasuwa da masana'antu da tsoffin manyan jami'an Sin da Amurka a nan birnin Beijing daga jiya Talata zuwa yau Laraba. Taron da ya samu halartar shugabannin Sin da Amurka a fannin kasuwanci da masana'antu da tsoffin manyan jami'ai da masana, wadanda suka tattauna tare da yin musanyar ra'ayi kan manufofi da matakan da kasashen biyu za su dauka nan gaba, shawarar 'zirin daya da hanya daya', kasuwanci ta yanar gizo, kimiyya ta zamani da dai sauransu.
A jawabinsa na bude taron, shugaban cibiyar musanyar tattalin arzikin kasar Sin Zeng Peiyan ya bayyana cewa, yana fatan 'yan kasuwan kasashen biyu za su kara tuntubar juna, ta yadda za su ba da gudunmawa, da kawar da banbancin ra'ayi, ta yadda nan gaba bangarorin biyu za su ciyar da harkokinsu na cinikaya da tattalin arziki.
Shugaban kungiyar 'yan kasuwa da masana'antu ta kasar Amurka Thomas Donohue ya bayyana imanin cewa, ya kamata Sin da Amurka su mai da hankali kan budewa juna kofa don cin moriyar juna a maimakon sakawa juna kangiya. (Amina Xu)