Sin na da karfin tinkarar matsalar cinikin dake tsakanin Sin da Amurka
Mataimakin direktan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na Sin Lian Weiliang ya bayyana yau, cewar Amurka ta kara yawan haraji kan kayayyakin Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 200, hakan zai kawo tasiri ga ci gaban tattalin arzikin Sin. Koda ba a iya magance hakan ba, amma shi ba babbar matsala ba ce ga Sin. Sin na da karfin tinkarar matsalar ta hanyar fadada bukatun cikin gida da kyautata ingancin bunkasuwarta. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku