Jami'an kungiyoyin biyu dai sun bayyana hakan ne, bayan ziyarar ganawa da masu ruwa da tsaki da suka kai kasar tsakanin ranekun 7 zuwa 9 ga watan nan na Oktoba, inda suka tattauna da wakilan gwamnati, da na mata, da jam'iyyun gama kai da 'yan jarida, game da yarjejeniyar da aka cimma.
Da suke yi wa manema labarai karin haske, game da sakamakon ziyarar tasu a helkwatar AU dake birnin Addis Ababan kasar Habasha, wakilan AU da na MDDr, sun bayyana kwarin gwiwar da suke da shi, game da tabbatar da cimma nasarar yarjejeniyar.
Wakilan sun ce, yana da matukar muhimmanci a shigar da dukkanin sassan Sudan ta kudu, cikin aikin wanzar da zaman lafiya, musamman ma mata. Sun kuma sha alwashi ci gaba da aiki tare da kungiyar IGAD ta raya kasashen gabashin Afirka, da sauran kungiyoyin kasa da kasa domin cimma nasarar da aka sanya gaba.
Yanzu haka Sudan ta Kudu ta shiga shekara ta 5 tana fama da yakin basasa, tun bayan barkewarsa a karshen shekarar 2013. (Saminu Hassan)