Sai dai kuma gwamnati da 'yan adawa na zargin juna da tayar da sabon fadan a sassan Kajo-Keji da Lainya.
Mataimakin mai magana da yawun sojojin babban kungiyar 'yan adawa kwatar 'yancin al'ummar Sudan (SPLA-I0) Lam Paul Gabriel, ya zargi dakarun gwamnati da fara kaiwa sansanoninsu hari a ranar Laraba, ranar da bangarorin da ba sa ga maciji da juna suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar.
Ya ce, fadan ya ci gaba har zuwa ranar Jumma'ar da ta gabata, kuma an kashe a kalla sojojin gwamnati 8 yayin bata kashin na kwanaki uku, sai dai ba a tabbatar da wannan ikirarin ba.
Amma kuma mai magana da yawun sojojin gwamnati Lul Roai Koang ya karyata zargin 'yan adawar, yana mai cewa, farfaganda ce kawai. Yana mai cewa, 'yan tawayen ne suka fara tayar da fadan a yankunan kudanci da arewacin kasar, a kokarin da suke na kara kwace yankuna domin girke dakarunsu. (Ibrahim)