Ministan lafiyar kasar Riek Gai Kok ya fadawa manema labarai cewa, gwamnatin kasar ta hada wata tawagar hadin gwiwa wajen sanya ido don kaucewa bazuwar cutar a wasu muhimman mashigar dake tsakanin kan iyakarta da DRC.
Yace gwamnatin kasar ta kafa wata tawagar jami'ai da suka hada da jami'an hukumar lafiya ta duniya (WHO) da sauran hukumomin bada agaji domin su tsara wani shirin daukin gaggawa ga duk wani mutum da ake zargin yana dauke da kwayar cutar ta Ebola a kasar ta gabashin Afrika mai fama da tashe tashen hankula.
Duk da irin tabarbarewar tsaro da ya daidaita kasar ta Sudan ta kudu tun a shekarar 2013, Kok yace, kasar a shirye take ta tinkari barazanar barkewar wata cuta tare da hadin gwiwar wasu hukumomin bada agaji.
Evans Liyosi, wakilin hukumar WHO a Sudan ta kudu, yace kasar Sudan ta kudu tana da kusanci da DRC inda aka samu bullar cutar a kwanan nan, don haka abu ne mai matukar muhimmanci a dauki matakan kariya daga cutar.