Ministan man fetur da iskar gas na Sudan, Azhari Abdul-Ghadir, wanda ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a jiya Lahadi, ya ce an dawo da fara aikin ne a ranar Asabar da ta gabata.
Ya ce an fara hakar man ne a rijiyar mai ta Toma ta kudu na kasar Sudan ta Kudu, da gangar danyen mai 20,000 a kowacce rana.
Ministan na sa ran adadin da ake samarwa ya kai ganga 80,000 a kowacce rana, idan aka fara aiki a rijiyoyi 5 da aka rufe a baya, tare da kammala gyare-gyare zuwa karshen shekarar nan.
Ya yi bayanin cewa, a yanzu jimilar man da Sudan ta kudu ke samarwa ya tsaya ne kan ganga 130,000 a rana, inda ya ce ana sa ran ya kai ganga 210,000 a kowacce rana ya zuwa karshen bana.
Sudan ta kudu dai na fitar da man da take samarwa zuwa kasuwanni duniya ne bisa amfani da batutan mai na kasar Sudan.
Sudan ta kudu na fama da yakin basasar da ya haddasa rufe aikin hakar man fetur, wanda shi ne jigon arzikin kasar. (Fa'iza Mustapha)