An jiyo Manawa Peter, kakakin kungiyar fafutukar 'yantar da al'ummar Sudan ta kudu yana cewa, taron ya shafi tattauna batun samar da kyakkyawan yanayi ne a kasar wanda hakan zai bada dama ga shugabannin siyasar kasar wajen shiga a dama da su shirin wanzar da zaman lafiyar kasar.
Ya ce Kiir ya nanata muhimmancin tura mayakan 'yan tawaye na SPLM-IO dasu shiga yarjejejniyar zaman lafiyar.
Kirr ya aikewa Machar goron gayyata, taron wanda zai gudana a Juba, babbam birnin kasar Sudan ta Kudu, kuma ana saran za'a sanya hannu kan yarjejeriyar zaman lafiyar, wanda ake saran mambobin kasashen gabashin Afrika IGAD za su halarta.(Ahmad)