Jakada James Morgan wanda ya bayyana hakan yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce, gagarumin rawar da kasar Sin take takawa a fannin samar da zaman lafiya, zai karfafawa bangarorin dake fada da juna a kasar rungumar zaman lafiya.
Jami'in ya ce, kasar Sin dai tana kira ne ga kowa da kowa ba tare da gindaya wani sharadi ba, da ya shiga shirin samar da zaman lafiyar. Haka kuma kasar Sin ba ta goyon kowane bangare a yakin basarar kasar,kana shirin samar da zaman lafiyar da take gudanarwa a kasar ya haifar da kyakkyawan sakamako.
Kasar Sudan ta kudu dai ta fada cikin tashin hankali ne a watan Disamban shekarar 2013, bayan da aka samu takaddamar siyasa tsakanin shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar, lamarin da ya raba kan sojojin kasar, har ta kai su ga gwabza fada.
Alkaluma na nuna cewa, yakin basasar kasar ya halaka dubban rayukan 'yan kasar baya ga miliyoyi da su ka bar muhallansu. (Ibrahim)