Da yake jawabi yayin ranar jami'an wanzar da zaman lafiya ta MDD karo na 70 a birnin Juba, mataimakin wakilin musaman na Sakatare Janar na MDD, kuma shugaban shirin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu, David Shearer, ya ce jami'an wanzar da zaman lafiya na fuskantar kalubale da dama a Sudan ta Kudu, amma duk da haka, suna jurewa, tare da ci gaba da bada goyon baya ga burin wanzar da zaman lafiya a kasar.
A don haka ya ce, su ke makokin abokan aikinsu, misali wadanda harin Mali na baya-bayan nan ya rutsa da su, da na Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da ma Sudan ta Kudu. Haka zalika, ya ce suna tunawa da jami'an UNMISS 55 da suka mutu a shekarar 2011.
David Shearer, ya ce hakkin shirin ne, kare rayukan fararen hula da taimakawa wajen wanzar da zaman lafiya mai karko a Sudan ta Kudu. (Fa'iza Mustapha)