UNMISS ta ce ta dauki wannan mataki ba tare da bata lokaci ba, inda ta kwashe jami'an rundunar 'yan sandan Ghanan (FPU) su 46 daga wajen da suke aiki a sansanin kare fararen hula na MDD PoC dake arewa maso yammacin Sudan ta kudu a ranar 8 ga watan nan na Fabrairu, a lokacin da aka gabatar da korafe korafe kan jami'an.
A wata sanarwa da aka fitar a Juba, babban birnin kasar Sudan ta kudun ta nuna cewa, an riga an kwashe tawagar jami'an 'yan sandan daga Wau zuwa wani sansani dake Juba.
Sanarwar tace, UNMISS ba zata taba lamintar duk wani batu da ya shafi cin zarafi ko aikata lalata ba.
Kana babban abinda UNMISS ta sa a gaba shine, ta bi diddigin laifukan da ake zargi da kuma yin adalci wajen daukar matakan ladaftarwa ga dukkan wadan da aka samu da hannu wajen aikata laifukan.
A cewar UNMISS, ta samu korafi kan zargin jami'an 'yan sandan na Ghana ne da hannu wajen aikata laifin cin zarafin mata a sansanin kare fararen hular dake Wau tun a ranar 8 ga watan Fabrairu.(Ahmad Fagam)