Shugaban Tarayyar Afrika Paul Kagame, ya ce mambobin kungiyar 49 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa yankin ciniki cikin 'yanci na nahiyar Afrika.
Paul Kagame, wanda kuma shi ne shugaban kasar Rwanda, ya sanar da hakan ne jiya a birnin Nouakchott, yayin bikin rufe taro karo na 31 na Tarayyar Afrika mai kasashe mambobi 55.
Kasashen Afrika ta kudu da Sierra Leone da Namibia da Lesotho da Burundi ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a Nouakchott. Inda Chadi da Swaziland kuma suka amince da aiki da yarjejeniyar bayan sun rattaba hannu kan ta a baya, abun da ya kawo adadin kasashen da suka amince da aiki da ita zuwa 6.
Ana bukatar adadin mafi karanci na kasashe 22 da za su rattaba hannu kan yarjejeniyar, sannan su amince da aiki da ita domin ba ta damar fara aiki, yayin da ake bukatar kasashe adadin kasashe 15 domin fara amfani da tsarin zirga-zirgar mutane da zama da aiki a wata kasa cikin 'yanci.
A cewar AU, yankin ciniki cikin 'yanci na nahiyar Afrika zai zama yankin cinikayya mafi girma, tun bayan kafuwar hukumar cinikayya ta duniya. Kuma zai samar da kasuwar da za ta kunshi mutane sama da biliyan 1.2 da alkaluman GDP da ya kai dala triliyan 2.5. (Fa'iza Mustapha)