Ya bayyana a ranar 29 ga wata cewa, bai dace a yi kariyar ciniki ba, kuma bai kamata kasar da ta samu ci gaba, ta shigar da kanta cikin yakin ciniki ba. Ya ce, idan Amurka ta ci gaba da rufe kofarta ga kasashen waje, matakin zai haddasa mata mummunar matsala.
Tawagar siyasa mai taken "Koch Network" dake karkashin jagorancin Charles G. Koch, na daya daga cikin masu goyon baya mafi karfi ga harkokin siyasar jam'iyyar Republic ta kasar Amurka, amma a baya-bayan nan, ta sha nuna rashin amincewarta da manufofin ciniki na gwamnatin Trump.
Bugu da kari, a watan Yunin na bana, tawagar ta tsara wani aikin lallashi wanda zai kashe dallar Amurka sama da miliyan 1 da kuma shekaru da dama, domin nuna kiyaya kan manufar kara harajin kwastan da gwamnatin Trump ta fidda. (Maryam)