Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Ma Zhaoxu ya shaidawa taron shugabannin dandalin siyasa game da shirin ci gaba mai dorewa na shekarar 2018 da MDD ta gudanar a birnin New York, cewa, ya kamata kasashe daban-daban su goyi bayan manufar tattauna batun tsakanin bangarori da dama da kiyaye tsari da ka'idar yin ciniki tsakanin bangarori da dama.
A wannan rana kuma, kungiyar sa kaimi ga yin mu'ammala tsakanin kasashe daban-daban mai zaman kanta ta kasar Sin da kamfanin Mercy Corps na Amurka sun shirya wani taron tattauna kan matsayin da Sin ke dauka a dangantakar abota wajen samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya mai dorewa.
A jawabin da ya gabatar Mr Ma Zhaoxu ya ce, kamata ya yi kasashen duniya su dukufa wajen kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan Bil Adama, da rage talauci, da raya dangantakar abota da kuma kyautata yanayin samun bunkasuwar kasa da kasa, ta yadda jama'arsu za su amfana daga bunkasuwar tattalin arzikin duniya cikin adalci.
Hakazalika, Ma Zhaoxu ya nuna cewa, a hanlin yanzu, ana fuskantar takardamar ciniki mai tsakani, abin da ya kara haifar da rashin daidaito da tabbaci ga tattalin arzikin duniya.
Amurka ce ta tayar da yakin ciniki mai girma a tarihi, kuma ta sabawa ka'idar ciniki ta kasa da kasa, matakin da zai kawo cikas ga tsarin cinikayyar duniya baki daya har ma zai girgiza kasuwannin duniya da hana farfadowar tattalin arzikin duniya. Ya kamata, kasashen daban-daban su kiyaye manufar tattaunawa tsakanin bangarori daban-daban, da kiyaye yin ciniki tsakanin bangarori daban-daban, da kuma yaki da kowace irin manufar ba da kariyar ciniki da kiyaye yin ciniki cikin 'yanci tsakanin bangarori da dama, in ji jami'in kasar ta Sin. (Amina Xu)