Asusun na IMF ya yi bayani cewa, kasar Sin ta samu ci gaba a wasu muhimman fannoni, sakamakon kwaskwarimar da ta yi a cikin gida. Kuma gyare-gyaren da ta yi kan ayyukan sa ido ya taimaka wajen rage kabubaloli ta fuskar sha'anin kudi. Sa'an nan, ta ci gaba da rage samar da kayayyakin da suka zarta bukatun a'umma, da kuma inganta ayyukan kare muhalli, da gaggauta ayyukan bude kofa ga waje.
Haka kuma, ya ce, kasar Sin tana cikin lokaci mai muhimmanci, cikin shekaru da dama da suka gabata, kasar Sin ta yi ta samun karuwar tattalin arziki da sauri, a halin yanzu kuma, ta fara mai da hankali kan ingancin kayayyaki. Kana, yadda take aiwatar da wannan sauyi, zai taimaka matuka ga bunkasuwar kasar Sin baki daya cikin shekaru da dama masu zuwa. (Maryam)