Masanin ya ce, nahiyar Afirka tana da damar inganta hanyoyinta na samar da abinci ta hanyar cikakkun alakamun yanayi da aka tattara ta hanyoyin zamani.
Ya lura da dewa, duk da ci gaban aikin gona da aka samu a nahiyar a 'yan shekarun nan, har yanzu wasu yankunan sun sha gabanta.
Chengula ya ce, yanzu haka mutum daya cikin mutane hudu a kasashen Afirka dake yankin Sahara yana fama da matsanancin karancin abinci mai gina jiki. Kana a 'yan shekarun dake tafe tsarin samar da abincin nahiyar zai ci gaba da fuskantar matsalin lamba, sakamakon karuwar yawan al'ummar da aka yi kiyasin za ta karu zuwa miliyan 1.3 nan da shekarar 2050.
Ya kuma buga misali da tsarin samar da rancen motocin noma ga manoma ta wayar salula mai suna "Hello Tractor" da aka farfado a kasashen Nijeriya da Kenya cikin farashi mai sauki, tsarin da rahotanni ke cewa ya baiwa manoman damar samun karin kaso 200 cikin 100 na amfanin da suke nomawa. (Ibrahim)