Jami'in na IMF wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taron bitar asusun na shekara-sherkara game da yanayin tattalin arzikin kasar Sin, ya ce sashen harkokin kudin kasar ba ya fuskantar wani hadari, biyo bayan kwararan matakan da gwamnati ta dauka, da raguwar karuwar basussuka, da ci gaban da aka samu wajen rage kayayyakin da ake samarwa fiye da kima, da karfafa matakan yaki da gurbata muhalli, ana kuma ci gaba da aiwatar da manufar bude kofa.
Daga ranar 17 zuwa 30 ga watan Mayun wannan shekara ce, wata tawagar asusun na IMF karkashin jagorancin James Daniel suka ziyarci Beijing da Shenzhen, domin gudanar da taron bitar asusun na shekara-shekara, inda suka yi hasashen bunkasar tattalin arzikin kasar ta Sin zuwa kaso 6.6 cikin 100 a wannan shekara da muke ciki, baya ga matsakaicin ci gaba na kaso 5.5 cikin 100 da zai samu nan da shekarar 2023.
Ya ce, babu tantama kasar Sin za ta kartata ga tsarin samun ci gaba mai dorewa, ganin yadda manufarta na yin gyare-gyare ta samu nasara ckin shekaru 30 din da suka gabata, da ma yadda mahukuntan kasar suka himmantu wajen ganin sun cimma wannan buri. (Ibrahim)