A ranar 21 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Dakar da nufin fara ziyara a kasar Senegal. Bangarori daban daban na kasar Senegal sun yi bayani game da ziyarar ta shugaba Xi.
Jarida mafi girma ta kasar Senegal "Le Soleil" ta gabatar da bayani na musamman a ranar 20 ga wannan wata, inda aka bayyana yanayin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Senegal a dukkan fannoni. Jaridar ta bayyana cewa, ziyarar shugaba Xi Jinping a wannan karo za ta sa kaimi ga raya dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu.
Shugaban kwalejin Confucius na jami'ar Dakar Mamadou Fall ya bayyana cewa, baya ga bunkasuwar tattalin arziki da kimiyya da fasaha, ya kamata a koyi kasar Sin a fannin raya al'adu.
Tashar internet mafi girma ta birnin Dakar wato seneweb.com ta wallafa labarai game da ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar Senegal a wannan karo a shafinta na farko. (Zainab)