Shugaba Xi ya bayyana kasar a matsayin zangon farko na ziyarar sa a ketare, tun bayan sake zaben sa a matsayin shugaban kasar Sin. Ya ce Sin na dora muhimmancin gaske game da kawance dake tsakanin ta da hadaddiyar daular Larabawa.
Ya kuma kara da cewa, irin kyakkyawar tarba da ya samu daga isar sa masarautar, ta tabbatar masa da irin karfin kawance, da dangantaka dake tsakanin kasar sa da hadaddiyar daular Larabawa, lamarin da ya yi matukar faranta masa rai.
Kaza lika shugaba Xi ya bayyana fatan ci gaba da zurfafa musayar ra'ayoyi bisa manyan tsare tsaren hadin gwiwa, tsakanin shugabanin sassan biyu. Ya kuma bayyana kwarin gwiwar samun nasarar ziyarar tasa ta wannan karo, da ma burin sassan biyu na karfafa zumuncin dake akwai tsakanin kasashen biyu da ma al'ummun su.
A nasu bangaren, mataimakin shugaban hadaddiyar daular Larabawa, da kuma yariman masarautar, sun yiwa shugaba Xi kyakkyawar tarba, suna masu bayyana shugaban a matsayin dadadden aboki kuma aminin kasar. Sun kuma bayyana zabar kasar a matsayin zangon ziyarar sa na farko tun bayan sake zaben sa shugaban Sin, a matsayin girmamawa ta musamman ga hadaddiyar daular Larabawa. (Saminu)