A gabannin ziyarar, jakadan kasar Sin dake Senegal Zhang Xun ya gana da manema labarun kasar Sin, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta zabi kasar Senegal a matsayin zangon farko na ziyarar aiki a Afirka, wannan ya nuna cewa, shugaba Xi da kasarsa sun dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakanin Sin da Senegal. Jakadan ya nuna imanin cewa, ziyarar za ta ciyar da dangantakar abokantaka ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni gaba, kana za ta kara samar da alheri ga jama'ar kasashen biyu. (Bilkisu)