Shugaba Xi ya ce, ta hanyar ziyarar da ya kai a UAE, bangarorin biyu sun yi nasarar cimma sabuwar matsaya, ya kara da cewa, yana da kyakkyawan kwarin gwiwa cewa muhimmiyar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana da ingantacciyar makoma.
Shugaban na kasar Sin ya ce, ya kamata kasashen biyu su zurfafa hadin gwiwarsu a dukkan fannoni, kana su gina tubalin bunkasuwar alakawar dake tsakaninsu da samar da cigaban bangarorin na dogon zango.
A nasa bangaren, sarki Mohammed bin Zayed ya ce, a shirye hadaddiyar daular Larabawa take ta kasance babbar aminyar kasar Sin mafi girma a yankin gabas ta tsakiya, da kuma yin hadin gwiwa wajen aiwatar da muhimman yarjejeniyoyin da aka cimma matsaya kansu a lokacin ziyarar shugaba Xi, kana da cigaba da karfafa mu'amalar hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu daga dukkan fannoni. (Ahmad)