Hukumar ta ce hadarin kamuwa da cutar ga masu shiga kasar ba shi da yawa, domin mutane kan kamu da ita ne bayan sun fara fama da alamomin da suka hada da zazzabi da rashin kwarin jiki da ciwon damatsa da na makwogwaro.
Hukumar ta shawarci masu tafiya kasar, su tuntubi likita a kalla makonni 4 zuwa 8 kafin tafiyarsu. Inda ta ce ya kamata tuntubar ta kunshi bayanai game da muhimman haduran lafiya da za a iya gamuwa da su, da tantance bukatar rigakafi da na maganin zazzabin cizon sauro da kuma gano ko akwai wasu kayayyakin lafiya da ake bukatar matafiyi ya dauka. (Fa'iza Mustapha)