Wannan na kunshe ne cikin rahoton da Mujjalar The Lancet ta wallafa a jiya, wanda sakamako ne na bincike da ta aiwatar a baya-bayan nan.
Binciken wanda Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta dauki nauyi, shi ne ya yi kiyasin kudaden da za a kashe da kuma moriyar da za a samu na fadada harkokin kiwon lafiya, domin cimma muradun ci gaba masu dorewa 16 na kiwon lafiya a wadancan kasashe 67.
Ayyukan za su kare mutuwar kuruciya da kusan miliyan 97 a duniya daga yanzu zuwa shekarar 2030.
Yayin da galibin kasashe za su iya bayar da kudin da ake bukata, matalautan kasashe za su bukaci taimako don cimma wannan bukata.
Darakta Janar na WHO Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce kula da kiwon lafiya ta bai daya ba zabi ba ne, hakki ne da ya rataya a wuyan kowacce kasa da gwamnati. (Fa'iza Mustapha)