Taken ranar yaki da cutar daji ta duniya na bana shi ne "Mun iya, Na iya", a hakika shi ne wani shiri na tsawon shekaru 3 wato daga shekarar 2016 zuwa 2018, an yi kira ga kowane mutum da ya samar da gudummawa wajen yaki da cutar daji don rage yawan mutanen da suka kamu da cutar a duniya.
Kawancen yaki da cutar daji na duniya ya gabatar da sanarwa a kwanakin baya cewa, yana fatan yin amfani da damar ranar yaki da cutar daji ta duniya wajen sa kaimi ga mutane da su yi bincike da samun jinya kan cutar daji a matakai na daidaiku, ta haka za a iya ceto karin rayukan mutane a duniya. (Zainab)