in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya: Kasar Sin za ta cimma nasarar manufofin ci gaba mai dorewa ta hanyar shirinta na yin gyare-gyare
2018-02-22 20:15:41 cri
Wani sabon rahoto da bankin duniya ya fitar ya bayyana cewa, shirin yin gyare-gyare da kasar Sin take aiwatarwa zai kara ba ta nasarar samun ci gaba mai dorewa har ma ta magance kalubalen bunkasuwa da take fuskanta.

Rahoton ya kara da cewa, ci gaban da kasar ta samu na tafiya kamar yadda ake fata, kana tattalin arzikinta zai ci gaba da daidaita yadda ya kamata. Sannan ci gaban da ta samu zai taka muhimmiyar rawa a kokarin da mahukuntan kasar ta Sin ke yi na cimma nasarar manufofin bunkasuwa.

Bugu da kari, rahoton ya ce manufofin da kasar Sin ta bullo da su game da kara samar da kayayyaki ta hanyar kirkire-kirkire, da takara tsakanin kasuwanni yayin da su ma sassa masu zaman kansu za su taimaka wajen cimma wadannan manufofi.

Jagoran tsara manufofin tattalin arziki na bankin duniya dake kasar Sin, Hoon S. Soh, ya bayyana cewa, gagarumin nasarar da kasar Sin ta samu a fannin kawar da talauci, ya taimaka matuka wajen rage matsalar kangin talauci dake ake fuskanta a duniya. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China