Bankin duniya ya yi hasashen cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin ta kai kashi 6.8 cikin dari a shekarar 2017, wato karuwar kashi 0.3 bisa kan hasashen da ya yi a watan Yunin bara. A shekarar 2018 kuma, karuwar za ta kai kashi 6.4 cikin dari, wato karuwar kaso 0.1 bisa hasashen bara. A shekarar 2019, tattalin arzikin kasar ta Sin zai karu da kashi 6.3 cikin dari, wanda ya yi daidai da hasashen da ya yi a watan Yunin bara. (Bilkisu)